Nayi Nadamar Shiga Harkar Film Inji Baba Karami

 


Nayi Nadamar Shiga Harkar Film, Gashi Larura ta Sameni Kowa Ya Gujeni, Inji Jarumi Baba Karami.

Jarumin ya bayyana hakan ne biyo bayan wasu abubuwa da suka faru dashi a yan kwanakin nan inda yayi fama da rashin lafiya har ta kai ga ya rame wanda ganin bidiyon shi a kwanakin baya ya saka jama'a maganganu da dama inda suke tambayar abunda ke damunshi.


Sai dai yace tunda yayi rashin lafiya babu wani jarumi ko wata jarumar da ta taimaka masa don yayi jinyar jikinsa a Kannywood hasalima wasu dariya suke masa wannan abun yasa shi yayi nadama kwarai da yin harkar film


Kamar yadda king indara ya wallafa, jarumin yace ya bawa masana'antar lokacin sa da dukiyar sa amma gashi abunda ya biyo baya dashi.


Har yan zu babu wanda yayi martani a bangaren jaruman kannywood din duk da cewa sunada halin da zasu  iya taimakawa domin ganin ya samu saukin halin da yake ciki.


#kannywoodNews 


Comments

Popular posts from this blog

Jaruma Fati Bararoji Ta Jawo Cece-kuce Kwanan Nan