Mansura Isah Na Cikin Damuwa Saboda Mutuwar Wata

 


Jarumar tace tabbas taji mutuwar baba saude saboda yadda tayi niyar taimaka mata, ganin halin da take ciki tace wallahi an fada mata cewa baiwar Allah zata mutu saboda cutar da take dauke dashi amma duk da haka tayi ta kokarin ganin ta nema mata magani ko dan tayi mutuwa mai salama cikin sauki.



Tace daman duk maganin da take nema mata tana nema mata ne dan ta samu nitsuwa ta kuma samu bacci koda mutuwa ya zo mata ya zo mata da sauki.



Jarumar ta bayyana irin ciwon dake damun baba saude, tace ciwon kansa ne kuma har ya riga da ya kamata sosai ta yadda babu mafuta sai dai mutuwa, duk da rayuwa da mutuwa duka na Allah ne.



Tabbas mansura isah tayi niyar taimakawa baba saude amma rai yayi halinsa mutuwa yazo, daga karshe tayi addu'ar Allah ya bata lafiya kuma tayi kira da duk wanda ke fama da ciwon kansa da yayi kokari yaje zuwa asibiti saboda ciwon kansa mugun ciwo ne.


Allah ka datar damu

Comments

Popular posts from this blog

Jaruma Fati Bararoji Ta Jawo Cece-kuce Kwanan Nan