Jodha Sabon Film Din Mansura Isah Yana Gab Da Kada Tarihi
Jaruma mansura isah tana gab da kafa tarihi a masana’antar Kannywood inda ta zo da wani sabon salo na film mai matukar tasiri da daukan hankalin jama'a, jaruma tayi amfani da wasu abubuwan suke faruwa a yanzu wanda yake shafar uwa da danta ko yarta, sannan tayi amfani da kwarewa.
Da farko an kashewa film din makudan kudi kuma anyi amfani da kayan aiki na zamani sannan anyi amfani da wasu abubuwa da suka zama kamar na gaske, inda jarumar ma ta futo ta bayyana yadda ta kone lokacin da ake saka mata wasu chemical a jikinta.
Kamar yadda zaku gani a bidiyon nan:
Jarumar ta sake bayyana yadda takeji akan film din inda tace tana ganin wannan film din zai zama makura kuma babban shirin da zai kafa tarihi a masana’antar Kannywood.
Jaruma mansura tun bayan da aurenta ya mutu tayi kokarin ganin ta kafa kanta kuma tayi amfani da damar ta akan wayar kan al umma akan yadda ake cin mutuncin mata da kuma yara kanana, wannan kyakyawan abu ne kuma abun mai kyau musanman ga mutanen mu na arewa.
Inda ake cin zarafin yaya mata, da yara kanana tace ta taba fuskantar irin haka shiyasa take kokarin ganin tayi iya yin ta don ganin ta kawo sauyi


Comments
Post a Comment