Hotunan Tsaraici: Jarumar Kannywood Ta Jawo Cece-kuce.
Jarumar tana daya daga cikin jaruman Kannywood sai dai ba kowa bane ya san fuskarta kasancewar bata cika futowa acikin fina finan Hausa ba. Sai dai tana yawan bibiyar daraktoci da kuma furodusoshin kannywood.
Fatima tahir saraki tana matukar shaawar harkar film kasancewar ta taso da kaunar abun a ranta, inda ta soma da kulla kawance da wasu daga cikin jaruman Kannywood musamman bilkisu salis, momee gombe da sauransu, sannan daga bangaren maza tana yawan bibiyar Abubakar bashir mai shadda da kuma sheikh isah alolo.
Jarumar Ta wallafa wasu hotuna masu cike da bayyana tsaraici da kuma saba dokar censorship board (hukumar tace fina-finai da dabi'a ta jahar kano), kamar yadda suka bayyana hakan a lokacin da suka dakatar da samha m inuwa daga futowa daga cikin ko wanne irin film a masana’antar.
Mutane sun zargi jaruman da lalata tarbiyar yara da kuma yin kokarin kawo wata dabi'a take kama da na Yahudawa inda a yanzu acikin kaso 100 na jaruman kannywood kaso kadan ne basu bayyana tsaraicin ba, musanman kirjin su, abun ya soma karfi ne tun lokacin da akayi bikin daida kahutu rarara.
Sai gashi yanzu jaruman sun samu sabuwar dabara tun zuwan tiktok inda yanzu karfi da yaji suke neman followers sosai a shafukan domin ganin sun kafa kansu a wannan waje, koda ace sunyi wani abu na ta'bara ko kuma masana’antar ta kore su to zasu koma chan suci gaba da sheqe ayarsu tunda kasuwar chan ta kashe na nan.
Shiyasa a kullum akan rigima suke da junan su domin trending wanda daga baya kuma sai ka gansu tare su nuna komai ya wuce shi me zaku iya cewa akan hakan?.
Comments
Post a Comment